Ukraine ta kai wani gagarumin farmaki kasar Rasha da jirage marasa matuka akalla 34, yau Lahadi farmakin jirage marasa matuka mafi girma a babban birnin kasar tun farkon yakin da aka fara a 2022, lamarin da ya sa tilas aka dakatar da zurga-zurgar jiragen sama a babban filin jiragen sama a birnin Moscow.
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce na’urorin kare hare haren saman Rasha sun kakkabo wasu jirage marasa matukan 36 a wasu yankuna a yammacin Rasha cikin sa’o’I 3 kawai a yau Lahadi.
Hukumar zurga-zurgar jiragen saman kasar Rasha ta ce an dakatar da zirga-zirgar jirage 36, filin jirage dake Domodedovo, Sheremtyevo, da Zhukovsky amma sun ci gaba da harkokin su daga baya.
An samu rahoton cewa mutum daya ya jikkata a yankin Moscow.
Ukraine ta ce, ita ma Rasha ta kaddamar da hare haren jirage marasa matuka 145 cikin dare. Kyiv ta ce na’urorin kare hare haren saman ta sun kakkabo 62 daga cikin jirage marasa matukan.
Dandalin Mu Tattauna