ABUJA, NAJERIYA. —
Wakiliyar Muryar Amurka a Abuja, Medina Dauda ta jagoranci tattaunawa da baki guda uku. Turakin Dass Alhaji Sama'ila Sani, wanda ya ga zabukan Amurka a shekaru 15 da Danjuma Abdullahi, wanda yayi zama da karatu a Jihar Pensylvania har tswon shekaru 10, sai kuma shugabar Gidan telebijin mai zaman kansa mai na Zamani TV da Cibiyar Koyar da Aikin Jarida Zamani Media Institute a Kano Fatima Dabo.
Mahalarta Zauren sun yi bitar zaben Amurka da ya gudana inda tsohon Shugaban Kasa Donald Trump ya lashe zaben da rata mai yawa tsakanin sa da abokiyar karawar sa kuma Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris.
Sun baiyana irin Amurkan da suke so su gani a shekaru 4 masu zuwa.