Zazzafar mahawarar ta kwaure ne sa’ilin da direban Bolt din ya isa gidan dan majalisar sannan ya bukaci a biya shi kudin aikinsa.
Alex Mascot Ikwechegh ne dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Aba ta Arewa data Kudu karkashin inuwar jam’iyyar APGA.
Wani faifan bidiyo ya nado hoton Ikwechegh a fusace a cikin wani katafaren gida a wani yanki na babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Daga hirar da aka nada a faifan bidiyon daya karade kafafen sada zumunta, dan majalisar yayi odar dodon kodi ne daga wani mai kasuwancinsa wanda ya dauki hayar direban tasi din zamanin ta Bolt domin ya kai masa kayan.
Mahawara mai zafi ta kwaure lokacin da direban Bolt din, Stephen Abuwatseya, ya isa gidan dan majalisar tare da bukatar a biya shi kudin aikinsa.
An jiyo Ikwechegh cikin fushi yana cewa mai kasuwancin dodon kodin ta wayar tarho. “ta yaya zaka aiko min wannan sakaran yazo yace min wai ni ya kamata in zo in same shi a motarsa in karbi dodon kodin dana saya daga gareka? A Najeriya zan iya batar da wannan mutumin kuma babu abinda zai faru.” dan majalisar ya furtawa wanda yake zance da shi a wayar.
Bayan kammala waya da mai sayar da dodon kodin ne, Ikwechegh ya fuskanci Abuwatseya yace, “ba zaka samu ko sisi daga gare ni ba tunda baka da mutunci. zaka dandana kodarka, kuma zanyi maganinka.”
Dan majalisar na APGA ya cika alkawarin daya dauka inda ya zabgawa direban mari 2 kwarara a kumatunsa, wanda shi kuma bai ce uffan ba sa’ilin da ake cin zarafinsa.