A wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar SSANU, Muhammad Ibrahim, da sakatare janar na NASU Peters Adeyemi, kungiyoyin biyu sun ce abin takaici ne cewa duk da wa’adin da aka baiwa gwamnati, babu wani sakamako mai kyau da ya fito da aka samu.
A watan Satumbar da ya gabata ne mambobin kungiyoyin suka gudanar da zanga-zanga a harabar jami’o’in dake fadin Najeriya a yau Talata domin neman a biyasu kudaden albashin da suke bi bashi.
Fusatattun ma’aikatan na dauke da kwalaye masu dauke da mabambantan sakonni a lokacin da suke gudanar da maci a cikin harabar jami’o’in, inda suke kira ga gwamnatin tarayya ta sakar musu albashin da ta rike musu tare da aiwatar da sauran bukatunsu.
Dandalin Mu Tattauna