Kwallon Kafa: Najeriya Za Ta Kara Da Amurka A Wasan Kwata Fainal

FILES-FBL-FIFA-INDIA-AIFF

Tawagar kwallon kafar mata ‘yan kasa da shekaru 17 ta Najeriya, Flamingos, ta samu nasara akan mai masaukin baki Jamhuriyar Dominican da safiyar yau Laraba inda ta samu galaba 100 bisa 100 a wasan rukuni na gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 17 ta 2024 dake gudana.

Flamingos basu samu damar jefa kwallo a raga ba sai minti na 89 inda ‘yar wasar tsakiya Shakirat Moshood, wacce ta kwace kwallo daga yadi na 25 tare da doka wani bahagon bugun da ya fi karfin mai tsaron ragar Jamhuriyar Dominican.

‘Yan matan Najeriya sun tsare kwallon da Shakirat Moshood din ta zura wacce ta kasance ta 4 da ta ci a gasar .

A Asabar mai zuwa, Najeriya da Amurka za su sake karawa a fafatawar wasan kwata fainal da su ka taba yi a Indiya a shekarar 2022 lokacin da Najeriya ta samu galaba sakamakon bugu fenariti.