Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya sha alwashin daukar tsauraran matakai a kan mutanen da suka cinna wuta a kan sakatariyoyin kananan hukumomi 3 a jihar a jiya Litinin.
Ya sha alwashin cewa sabanin makamantan wannan lamari da ya faru a baya, ba za’a kyale hakan ta shude ba kuma gwamnatinsa za ta hada gwiwa da hukumomin tsaro wajen zakulo wadanda suka aikata aika-aikar tare da gurfanar dasu.
Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne a yayin da yake rantsar da sabbin kwamishinoni 4 a dakin taro na fadar gwamnatin dake birnin Fatakwal.
Ya kuma tunatar da mahalarta taron cewa tunda fari saida ya gargadi sabbin ciyamomin game da yiyuwar kai hare-haren, sannan ya yabawa magoya bayansa a kan yadda suka kai zuciya nesa lokacin hatsaniyar.