An Samu Wasu Fashewa A Sakatariyar Jam'iyyar APC Ta Jihar Ribas

Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)

A yau ne ake gudanar da zaben shugabannin kananan Hukumomi a jihar Ribas da ke kudacin Najeriya duk kuwa da Tirka Tirka da aka fuskanta kamin Ranar zabe, Inda aka Samu hukunce-hukunce daban daban daga kotu kan zaben.

Al’ummar jihar sun fito domin kada kuri’un su, inda aka samu fashewar wani abu a Hedikwatar Jamiiyar APC a jihar. Wasu al’ummomin jihar sun bayar da rahoton cewa ana gudanar da zabe lafiya a mazabunsu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta sanar da samun fashewa guda biyu a garin Fatakwal a yau, Asabar, 5 ga Oktoba, 2024.

An samu fashewar ta farko a sakatariyar jam'iyyar APC dake kan titin Aba da misalin karfe 3:00 na safe. Wani jami’in tsaro ya bayar da rahoton jin kara mai karfi. Fashewar ta yi mummunar barna, inda ta lalata kofar da kuma farfasa tagogin ginin.

Fashewar ta biyu ta faru ne a sakatariyar Majalisar Obio/Akpor . Shaidun gani da ido sun bayyana ganin wata bakar mota kirar Toyota Hilux da wata farar karamar mota kirar Toyota Sienna sun wuce ta sakatariyar da gudu. An yi zargin cewa mutanen da ke cikin wadannan motocin sun jefa wani abu ne, wanda ake zargin bam ne, wanda ya farfasa rufin tare da lalata gidan janareta ginin.

Rundunar da ke yaki da bama-bamai ta tattara samfura daga bangarorin biyu domin tantancewa, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo wadanda suka aikata wadannan munanan ayyuka. Rundunar ‘yan sandar jihar tayi kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga hukuma.

Sannan Rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar wa mazauna garin Fatakwal cewa suna daukar dukkan matakan da suka dace don inganta tsaro da tabbatar da tsaron al’ummar jihar.