Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Hana ‘Yan Sanda Shiga Zaben Kananan Hukumomin Ribas

'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da kakakinta, SP Grace Iringe-Koko, ta fitar mai taken: “zaben shugabannin kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 5 ga watan Oktoban da muke ciki.”

Rundunar ‘yan sandan Ribas ta bayyana cewa za ta aiwatar da umarnin kotu game da zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a fadin jihar a gobe Asabar.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da kakakinta, SP Grace Iringe-Koko, ta fitar mai taken: “zaben shugabannin kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 5 ga watan Oktoban da muke ciki.”

A cikin sanarwar, rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da samun umurnin kotun da ya hana ta gudanar da aikin tabbatar da tsaro yayin zaben kananan hukumomin.

Rundunar ta kara da cewa tana sane da hukuncin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta zartar na ranar 30 ga watan Satumbar da ya gabata wanda ya hana ta shiga a dama da ita a zaben.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sashen harkokin shari’a na rundunar ya ba da shawarar cewar hukuncin kotun na 30 ga watan Satumba yafi muhimmanci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG