Fusatattun masu zanga-zanga sun yiwa shelkwatar hukumar zaben jihar ribas (RSIEC) tsinke, suna rera wakokin cewar “wajibi ne a gudanar da zabe.”
Matasan dake zanga-zangar sun ce sun je ne su kare hukumar zaben da duk wani yunkuri na kawowa shirin zaben cikas.
Masu zanga-zangar sun bijirewa ruwan saman da ake zugawa a jihar sannan suka kakkafa rumfuna, a yayin da suke ci gaba da rera wakoki da kade-kade tare da toshe wane bangare na babbar hanya.
Wadanda suka halarci gangamin sun hada da Edison-Ehie, shugaban ma’aikatan fadar gwamnan, da Victor Oko-Jumbo, kakakin tsagin fubara na majalisar dokokin jihar da Sokari Goodboy, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ahoada ta Yamma.
Zanga-zangar ta samo asali ne bayan da gwamnan ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana cewa ya ziyarci hukumar zaben jihar (RSIEC) da karfe 1 na daren Juma’a, domin hana rundunar ‘yan sandan jihar Ribas mamaye harabarta.