Tsohon Zakaran NBA, Dikembe Mutombo, Ya Mutu Yana Da Shekaru 58.

  • VOA Hausa
Mutombo wanda aka haifa a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, da fari ya zo jami'ar Georgetown dake Washington ne a bisa tallafin karatu a shekarar 1987, sannan yayi shura sa'ilin daya shiga kungiyar wasan kwallon kwando yana shekararsa ta 2.

Tsohon zakaran wasan kwallon kwando, Dikembe Mutombo ya mutu yana da shekaru 58 da haihuwa bayan ya sha fama da sankarar kwakwalwa a yau Litinin, a cewar hukumar wasan kwallon kwando ta Amurka (NBA).

Mutombo wanda aka haifa a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, da fari ya zo jami'ar Georgetown dake Washington ne a bisa tallafin karatu a shekarar 1987, sannan yayi shura sa'ilin daya shiga kungiyar wasan kwallon kwando yana shekararsa ta 2.

A zaben 'yan wasan kwallon da NBA ta gudanar a 1991, kungiyar Denver Nuggets ta zabe shi a mataki na 4.

Bayan ga Nuggets, Mutombo ya yiwa kungiyoyin Atlanta Hawks, Philadelphia 76ers, New Jersey Net ta wancan lokacin da New York Knicks da kuma Houston Rockets wasa.

Baya ga fagen wasan kwallon kwando, Dikembe Mutombo ya yi suna a ayyukan bada agaji.

A1997, ya kafa Gidauniyar Dikembe Mutombo domin inganta harkokin ilmi da rayuwar al'ummar kasarsa ta Dr Congo.

A shekarar 2022, nba ta bayyana cewar Mutombo na samun kulawar likitoci akan larurar sankarar kwakwalwa a Atlanta.

Jaridar The League ta wallafa cewar ya mutu a kewaye da iyalansa a yau Litinin.