A jiya Laraba, masu shigar da kara a Jamhuriyar Benin suka bayyana cewa an kama mutane 3, ciki har da wani Kwamandan Askarawan Tsaron Fadar Shugaban Kasa, Djimon Dieudonne Tevoedjre, a bisa zarginsu da kitsa juyin mulki a kasar.
Sauran mutane 2 da ake tuhuma da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon sun hada da wani tsohon ministan wasannin kasar, Osward Homeky da wani dan kasuwa na hannun daman shugaban kasar, olivier boko.
Mai shigar da kara na musamman a kotun Jamhuriyar Benin mai hukunta laifuffukan da suka shafi kudi da ta’addanci, Elonm Mario Metonou, yace an shirya gudanar da juyin mulkin ne a gobe Juma’a.
A cewar kotun, an kama Homeky ne da misalin karfe dayan daren ranar Talata yayin da yake mika fiye da jakunkuna 6 makare da kudin CFA biliyan 1 da rabi (kwatankwacin dala miliyan 2 da rabi) ga kwamanda, Djimon Dieudonne Tevoedjre.