An Haife Ni Da Baiwar Zane-Zane Da Kayan Marmari -  Zainab Zakari

Zainab Zakari

Wata matashiyar mai suna Zainab Shu’aibu Zakari ta bayyana wa Muryar Amurka yadda ta gano cewa tana da baiwar zane-zane na sassaka da kayan marmari.

Zainab tace babu wanda ya koya mata, duk abinda take yi baiwane daga Allah, inda take zuwa kasuwar yan lemo da ke Kano ta sayo kankana ta zo gida ta fara sarrafa izuwa abubuwa daban daban ta hanyar sassaka da zane-zane.

Har ilayau Zainab tace tana da burin ganin ta koyar wa wadansu musamman matasa mata yadda zasu dauke shi a matsayin sana’a ta dogaro da kai.

Babu shakka irin wadannan labarai sun zama wasu abubuwa da ke karfafa ma masu baiwa irin Zainab a fannoni daban daban wajen tashi su bayyana hazakar su da amfani da baiwarsu wajen samar wa kai aikin yi da sana’a, harma da koyarwa wasu don su amfana.

Your browser doesn’t support HTML5

An Haife Ni Da Baiwar Zane-Zane Da Kayan Marmari -  Zainab Zakari