Paris 2024: An Hana ‘Yar Najeriya Damar Fafatawa A Gasar Tseren Mita 100

  • VOA Hausa

Favour Ofili

‘Yar tseren Najeriya, Favour Ofili, ta bayyana cewar ba za ta fafata a gasar tseren mita 100 a gasar Olympics ta birnin Paris ba saboda gazawa a fannin gudanarwa tsakanin hukumar kula da ‘yan wasan motsa jiki ta Najeriya da kwamitin shirya gasar Olympics ta kasar.

Da take bayyana takaicinta a jerin sakonnin X data wallafa a jiya Talata, Ofili ta tuhumi gaskiya da amanar hukumomin 2, sannan ta bukaci a gudanar da bincike a kan asarar wannan damar.

Ofili wacce tsohuwar ‘yar wasar guje-guje da tsalle-tsalle ce ta jami’ar jihar Legas ta bayyana fatan shigar da ita a gasar tseren mita 200.

An ruwaito abinda ta wallafa na cewar, “ina matukar takaicin cewar yanzun nan aka shaida mini cewar ba zan fafata a gasar tseren mita 100 ta wannan wasannin olympics ba. Na cancanta, amma jami’ai a hukumar AFN, mai kula da ‘yan wasan motsa jikin Najeriya da na kwamitin shirya gasar Olympic na Najeriya sun gaza shigar da suna na. Na yi aiki tsawon shekaru 4 domin samun dama. Don me haka zata faru?”

Duk da cewar ta cancanta ta fafata, Ofili ta bayyana cewar jami’an basu shigar da sunanta ba, matakin daya janyo maimaituwar irin abinda ya faru a gasar wasannin Olympics da ta gabata, ta birnin Tokyo a shekarar 2020.

Sai dai Ministan Bunkasa Wasannin Najeriya, Sanata John Owan Enoh, yace zai binciki yadda aka tsame sunan ‘yar wasan motsa jikin, daga gasar na bana dake gudana yanzu haka a birnin Paris.