Sakamakon amincewa da sabon mafi karancin albashi da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi, gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bada shawarwari akan mafi karancin albashi domin tsara yadda za a aiwatar da biyan naira dubu 70 kamar yadda aka cimma matsaya da hadaddiyar kungiyar kwadago.
Yayin bikin kaddamar da kwamitin, da mataimakin gwamnan kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya gudanar a madadin gwamnan, an jaddada hakkin da ya rataya a wuyan kwamitin na samar da tsarin da za’a yi amfani dashi wajen aiwwatar da biyan mafi karancin albashin ba tare da bata lokaci ba.
A cewar Gwarzo,” gwamnatinmu na baiwa batun walwalar ma’aikata mahimmancin gaske. Muna da yakinin cewar aiwatar da dokar sabon mafi karancin albashin zata inganta cigaban jihar kano ta kowanne fanni.”
An baiwa kwamitin, da zai kasance karkashin jagorancin mashawarcin gwamnan Kano na musamman akan al’amuran da suka shafi jihar kuma tsohon shugaban ma’aikata na jihar Kano, Alhaji Usman Muhammad, wa’adin makonni 3 ya gabatar da shawarwarinsa.
Mambobin kwamitin sun kunshi fitattun jami’an gwamnatin Kano da wakilai daga bangarori daban-daban:
– Alh. Abdullahi Musa, Shugaban Ma’aikata
– Alh. Ibrahim Jibril Fagge, Kwamishinan Kudi
– Alh. Musa Suleman Shanono, Kwamishinan Kasafi Da Tsare-Tsare
– Baba Halilu Dantiye, Kwamishinan Yada Labarai
– Comrade Baffa Sani Gaya
– Dr. Aliyu Isa Aliyu
– Salahudeen Habib Isa
– Ibrahim I. Boyi
– Ibrahim Muhammad Kabara
– Mustapha Nuraddeen Muhammad
– Abdulkadir Abdussalam
– Umar Muhammad Jalo
– Hassan Salisu Kofar Mata
– Yahaya Umar