Majalisar Dokokin Kasar Gambia Ta Haramta Yi Wa Mata Kaciya

Masu yaki da yi wa mata kaciya a kasar Gambiya

‘Yan majalisar dokokin Gambia sun amince da wasu shawarwari a jiya litinin, wanda ya haramta yi wa mata kaciya, bayan da aka kada kuri’a a karshen wannan watan kan ko za a sanya Al’adar a matsayin aikata laifi ko a’a.

Tun a shekara ta 2015 ne dai aka haramta yiwa mata kaciya a Gambia, amma tsarin al'adar da ke da tushe ya ci gaba da yaduwa a kasar da ke yammacin Afirka, kuma hukuncin farko da aka yanke a bara ya haifar da cece-kuce akan dokar.

Ku Duba Wannan Ma An Kama Wata Likita Mai Yi Wa Mata Kaciya A Amurka.

Bayan zazzafar muhawara a jiya litinin, kudirin da ke kunshe a cikin rahoton kwamitin hadin gwiwa na kiwon lafiya da jinsi ya zartas da cikakken zama a majalisar, inda ‘yan majalisa 35 suka kada kuri’ar amincewa da kudurin, yayinda 17 kuma suka ki amincewa, biyu kuma basu kada kuri’a ba.

A halin yanzu an sanya ranar 24 ga watan Yuli, a mastayin ranar da za a yanke hukuncin ko za a sanya kaciyar Mata a matsayin aikata laifi ko a’a.

Idan Majalisar dokokin kasar ta amince da hakan, Gambia za ta zama kasa ta farko da ta janye dokar hana kaciya. A watan Maris ne aka yi karatu na biyu inda ‘yan Majalisa biyar daga cikin 53 suka kada kuri’ar kin amincewa da shi, daya kuma ya ki kada kuri’a.

Wata mace da ta sami ciwon yoyon fitsari sakamakon yi mata kaciya

Bayan karatu na biyu, kwamitin hadin guiwa ya gudanar da taron tuntubar al'umma na kasa tare da shugabannin addini da na gargajiya, likitoci, wadanda abin ya shafa, kungiyoyin farar hula da masu kaciya da dai sauransu.

Sakamakon bincike da tuntubar da aka yi na nuni da cewa, duk nau'ikan yi wa mata kaciya cin zarafin mata ne mai ban tsoro na azabtarwa" da kuna nuwawa mata wariya.

“Sake dokar zai zama babban koma baya ga Gambia,” in ji Amadou Camara, dan majalisar da ya karanta rahoton.

Likitoci su na yi wa wata mace da aka yi wa kaciya aiki

Hukuncin FGM na farko a watan Agustan da ya gabata - na wasu mata uku da aka samu da laifin yi wa kananan yara mata takwas kaciya- ya harzuka al'umma,kuma ya sa dan majalisa mai zaman kansa Almaneh Gibba ya gabatar da kudirin soke dokar a watan Maris.

Gibba da masu mara masa baya wadanda suka hada da manyan malaman addini sun ce haramcin ya keta hakkin ‘yan kasar na gudanar da al’adu da addininsu a kasar da ke da rinjayen musulmi. Ra'ayin Limamai da dama basu yarda da wannan hujjar ba.

Masu zanga zangar yaki da kaciya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yi wa mata kaciya ba shi da wani fa'ida ga lafiya kuma yana iya haifar da zubar jini da yawa, firgita, matsalolin tunani har ma da mutuwa.