Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wata Likita Mai Yi Wa Mata Kaciya A Amurka.


FILE - A man's T-shirt reads "Stop the Cut" referring to Female Genital Mutilation during a social event advocating against such harmful practices at the Imbirikani Girls High School in Imbirikani, Kenya, April 21, 2016.
FILE - A man's T-shirt reads "Stop the Cut" referring to Female Genital Mutilation during a social event advocating against such harmful practices at the Imbirikani Girls High School in Imbirikani, Kenya, April 21, 2016.

An kama wata mace, likita a Amurka wacce ake zargin ta da yiwa yara 'kananan 'ýan mata 'yan tsakanin shekaru shida zuwa takwas kaciya, a shari’ar farko tun kafa dokar haramta wannan ta’asa a shekarar 1996.

Jumana Nagarwala, likita ce Yar shekaru 44 a Asibitin birnin Detroit, dake jihar Michigan, an same ta da laifin yiwa yara mata 'kanana kaciya tun kusan shekarar 2005, kamar yadda mai gabatar da karar kan manyan laifuka ya bada bayani a jiya Alhamis. Maikatar Shari’a ta Amurka tace matar ta aikata mummunan laifi akan wadanda bazasu iya kare kansu ba.”

An gabatar da Nagarwala a gaban kuliya a kotun yanki ta Detroit a jiya Alhamis inda aka bada umarnin kulleta sai ranar Litinin, domin cigaba da sauraron shari’ar da kuma irin laifukan da ake zarginta dasu, wand'anda suka hada da yi wa Yara 'kanana mata 'yan shekaru Bakwai kaciya a watan Fabrairu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG