Bayan ce-ce-ku-ce da muhawara da ƴan Najeriya ke tayi akan yarjejeniyar samoa da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu, wanda ake zargin akwai amincewa da auren jinsi cikin daftarin yarjejeniyar da zaisa ƙasar ta samu lamunin daloli masu yawa, gwamnatin tarayya ta musanta wannan zargi.
A hirarsa da Muryar Amurka, Ministan Kasafi Da Tsare-Tsare, Abubakar Bagudu, ya musanta wannan zargi, kuma yayi karin haske kan wannan batu, inda yace dama yarjejeniyar tana nan shekaru da dama da suka gabata.
Yanzu kuma sabunta yarjejeniyar akayi, kuma babu batun auren jinsi, halasta luwadi da maɗigo.
Bagudu ya kara da cewa, yarjejeniyar samoa, ta haɓaka tattalin arzikin kasa-da-kasa ne, ta hanyar cinikayya da dai sauransu.
Your browser doesn’t support HTML5