Mataimakin Shugaban Jami’ar wanda farfesa ne a fannin ilimin halitta da kwayoyin halittu, yana kan hanyar sa daga Sokoto zuwa Kaduna ne lokacin da 'yan bindigan suka kai hari su ka kashe shi a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.
Da yake tsokaci kan kisan, mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Suleiman Bilbis ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai rikon amana da addini, da kwazo, da jajircewa.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto jami’an tsaro ba su ce yi wani bayani ba da lamarin ba, sai dai Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta sanar da rasuwar a wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook da yammacin jiya Litinin cewa, “Mutuwar tasa babbar asara ce ga al’ummar jami’a da kuma duniyar ilimi. Allah ya karbi ransa, ya gafarta masa zunubansa, amma wannan rashi ne mai zafi ga daukacin jama'ar jami'a da kuma jami'a baki daya."
Ana ta aika sakonnin ta’aziya ga iyalan marigayin da kuma jami'ar Usmanu Danfodiyo kai tsaye da kuma ta kafofin sadarwa. Sheikh Abdurrahman Umar Bagarawa ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, “Wallahi na firgita da mutuwar nan!... Kwanaki uku da suka shige, nake maganarsa da Mal. Abdul-Alim Isa T/Mafara, har nake cewa ya turo min nambar wayarsa, ashe Allah bai nufa zamu yi ganawa ta karshe ba! Mutumin kirki da riko da addini. Allah ya gafarta masa!”
Shi kuwa Professa Isa Ali Pantami tsohon Ministan sadarwa cewa ya yi “Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalansa, VC, Farfesa Bilbis, al'ummar jami'a, 'yan uwa da abokan arziki, tare da addu'ar Allah Madaukakin Sarki ya shigar da shi Jannatul Firdausi.”
Dandalin yanar gizo na malaman jihar Katsina shi kuma ya wallafa cewa, “Allah ya karbi ransa ya gafarta masa zunubansa, amma wannan rashi ne mai radadi ga daukacin jama'ar jami'a da fannin ilimi baki daya. Allah ya jiqanshi ya karbi shahadarshi, Allah ya shiryi masu irin wannan aika-aikan, in ba masu shiryuwa bane, ya Allah ka hukunta su bisa qaddarawar ka ya Rabb Amin. Innalillahi Yanzu shike nan mutum mai amfani mai amfànar da Al'umma an kashe shi haka kawai?.”
A nata sakon jajen, kungiyar daliban sashen nazarin halittu ta wallafa cewa, “Hakika mun yi rashin uba da kuma mai ba da shawara a fannin ilimi Farfesa Yusuf Saidu DVC na fannin nazari da fasaha,kuma daya daga cikin kwararrun malamai da muke da su a sashen nazarin halittu da kwayoyin halitta da ke Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato. Ina rokon Allah Ta'ala Ya sa Jannatul Firdausi ce makomarsa ta karshe.”
Idan dai za a iya tunawa, wasu ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da wasu masu bautar kasa 12 a watan Agusta bara, da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Akwa Ibom a hanyar Gusau zuwa Funtua, kuma har yanzu daya daga cikinsu yana hannun 'yan ta'addar.