Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Shafe Shekaru Ana Fama Da Matsalar 'Yan Bindiga - Sarkin Musulmi


Yan bindiga
Yan bindiga

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin taron kolin zaman lafiya da tsaro a shiyar arewa maso yammacin Najeriya daya gudana a jihar Katsina.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, yace za'a shafe shekaru kafin shiyar arewa maso yammacin Najeriya ta fita daga matsalar 'yan bindiga.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin taron kolin zaman lafiya da tsaro a shiyar arewa maso yammacin Najeriya daya gudana a jihar Katsina.

Ya kara da cewar, "abinda ya zama wajibi a gare mu shine kalubalantar wadannan 'yan bindigar saboda dukkaninmu mun san illolin matsalar 'yan bindiga da masu tada kayar baya a rayuwarmu. Saidai za'a shafe shekaru kafin mu fita daga kangin 'yan bindigar idan ma har zamu iya fita"

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmin ya kuma bayyana aniyar sarakunan gargajiya ta yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro da gwamnonin shiyar arewa maso yamma su 7 domin ceto yankinmu daga kangin 'yan bindiga da masu tada kayar baya.

Sarkin Musulmin yayi amanar cewar a karshen taron, za'a samu shawarwari akan yadda za'a shawo kan matsalar rashin tsaro ta yadda al'umma zasu samu sukunin gudanar da harkokinsu cikin lumana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG