An kama wasu yara maza uku masu shekaru 11, 12 da 16 wadanda Hukumar FBI ta yi wa lakabi da "kananan fitinannu" da ake zargi da yin fashi a wani banki a Texas.
Ofishin FBI da ke Houston ya fada a wani sakon da ya wallafa a shafin X, ya ce an tuhumi yaran uku da laifin "fashi ta hanyar barazana."
An tsare kananan yaran da ba a bayyana sunayensu ba saboda shekarunasu.
Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta fitar da hoton wadanda ake zargin ne bayan fashin bankin da suka yi a ranar 14 ga watan Maris, inda ta kara da cewa "ko ku yarda ko ku bari, sun yi fashi ne a bankin Wells Fargo."
Ofishin ‘yan sanda na gundumar Harris ya fada wa talabijin ta KTRK cewa, yaran sun mika wata takarda mai dauke da rubutaccen barazana ga wani ma’aikacin banki sannan suka gudu da kafa da wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba.
Ofishin ya ce iyayen biyu daga cikin yaran wadanda da alama ba su yi kokarin sanya abin rufe fuska ba ko kuma boye sunayensu a yayin fashin ne suka shaidawa hukuma ko su wanene.
~ AFP