A wannan mako ne kafofin sadarwa ta dauki dumi bayan da al’ummar suka sami labarin cewar kotu ta bada belin fitattaciyar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya, wanda aka aiketa gidan gyaran hali har zuwa ranar 20 ga wannan wata domin sauraran kararta da al’ummar unguwar su suka shigar game da yada kalamanta ke bata tarbiyar wanda basu dace ba a kafar TikTok.
Muryar Amurka ta sami zantawa da Kakakin Kotuna ta jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, dangane da dalilin sake Murja duk da cewar kotu tun da farko ta ce ba za’a bada belinta ba sai yace
“Babu shakka an sake Murja kuma yana da kyau mutane su sani cewar aikin kotu shine ta gudanar da shari’a kowace iri ce mussamam ma na mai lafi idan aka gabatar gabanta, sannan kotu bangarori ne da dama suka hadu suka samar da ita
Ya ce akwai bangaren masu gabatar da kara, akwai na lauyoyin kariya sannan akwai bangaren shi alkalin.
An gabatar da ita inda bangaren da suka bayar da ita suka nemi da a basu belinta domin su cigaba da gudanar da bincike, inda suka ce akwai abinda ya kamata su bincika wanda basu kamala ba.
Wannan dalili ne ya sa kotu ta bada belinta har zuwa ranar da ta tanada domin cigaba da sauraron karar.
Bayan samun labarin ba da belin, kafafen sadarwa ya cika da jita-jitar cewar kwamandan Hisbah ya ajiye aikinsa sakamakon bada belin Murja Ibrahim Kunya da kotu ta yi.
Mun tuntubi hukumar ta Hisbah inda Mataimakiyar Kwamandan Hisbah, Dr Khadija Sagir Suleman, ta musanta hakan, tare da cewar wannan labarin ba haka yake ba ta kuma tabattar cewa Kwamandan Hisbah Shiek Aminu Ibrahim Daurawa yna nan kan aikinsa.
Ta kara da da cewar a bangaren hukumar ta Hisbah, sun gudanar da ayyukansu sun kuma mika ta ga kotu a halin da ake ciki zance na hannun kotu ta bar hannun hukumar ta Hisbah
Kamar yadda kakakin kotuna ya bayyana a ranar Talata ne kotu za ta cigaba da sauraren karar Murja kunya.
A saurari cikakken rahoton Baraka Bashir:
Your browser doesn’t support HTML5