Ofishin Jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ta fitar da wata shawara ga ‘yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta kudu kan zama gabanin wasan kusa da na karshe na gasar AFCON tsakanin tawagar Najeriya ta Super Eagles da Bafana-Bafana ta kasar Afrika ta Kudu.
Sanarwar da aka fitar a ranar Talata ta gargadi 'yan Najeriya mazauna kasar ta Afrika ta Kudu da suyi taka tsan-tsan da irin murnar da za suyi in har Najeriya ta samu nasara a wasan na ranar Laraba.
Sanarwar ta shawarci ‘yan Najeriya masu cirani a kasar ta Afrika ta Kudu da su rika lura da kalaman da suke furtawa, sannan kuma su lura da inda suka zabi kallon wasan, musamman a wuraren taruwar jama’a.
Ta kuma roki ‘yan Najeriya da su guji murna da bukukuwan tunzura jama’a da ka iya tada zaune tsaye idan har Najeriya ta yi nasara a wasan da za a fafata a ranar Laraban nan.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ademola Lookman ya zura kwallon da ta taimakawa Super Eagles samun damar tsallakewa zuwa matakin kusa da na karshe a gasar AFCON bayan ta doke Angola da ci 1-0 a wasan daf da na karshe.