Jiragen Ruwan China Da Rasha Za Su Iya Wucewa Ta Bahar Maliya Ba Tare Da Sun Fuskanci Wata Matsala Ba - Houthi

Kungiyar Houthi

Kungiyar ta Houthi ta ce suna nuna goyon bayansu ga Falasdinawa ne a daidai lokacin yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas a Gaza kuma sun kai hare-hare fiye da 30 a tekun Bahar Rum. 

Wani babban jami'in kungiyar 'yan ta'adda ta Houthi da ke samun goyon bayan Iran ya ce jiragen ruwan China da na Rasha za su iya wucewa ta Bahr Maliya ba tare da sun fuskanci wata matsala ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya rawaito cewar Mohammed al-Bukhaiti, wanda mamba ne na shugabancin ‘yan siyasar kungiyar Houthi, ya fada a wata hira da ya yi da kafar yada labaran Rasha ta Iz-ves-tia cewa, hanyoyin jigilar kayayyaki da ke kewayen kasar Yemen ba su da hadari ga jiragen ruwa daga kasashen China da Rasha matukar dai jiragen ba su da alaka da Isra'ila

Kungiyar ta Houthi ta ce suna nuna goyon bayansu ga Falasdinawa ne a daidai lokacin yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas a Gaza kuma sun kai hare-hare fiye da 30 a tekun Bahar Rum.

Sai dai 'yan kungiyar ta Houthi sun kaddamar da hare-hare kan jiragen ruwa da ba su da wata alaka da Isra'ila, lamarin da ya sa wasu kamfanonin sufurin jiragen ruwa ke kaucewa hanyoyin jigilar kayayyaki inda 'yan Houthi suka kaddamar da hare-haren.