Abuja, Najeriya —
Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo zuwa fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Wannan mataki ya biyo bayan cece-kucen da ya dabaibaye ma’aikatar kula da jin kai, musamman batun bayar da kudin kwangila na tuntuba da ya kai Naira miliyan 438 don shirin jinkai na kasa wa kamfanin New Planet Projects Ltd da yake da alaka da mallakar Ministan.