A ci gaba da bitar mahimman abubuwan da suka wakana a shekarar 2023 mai bankwana yau zamu nufi jamhuriyar Nijar wace ta fuskanci babbar dambarwa bayan da sojoji suka kifar da zabebben Shugaban Kasa Mohamed Bazoum a wani lokacin da ake ganin gwamnatinsa ta fara shimfida mulki mai kusanci da talakka.
Wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma ya yi mana bitar mahimman abubuwan da suka wakana a shekarar 2023 da wadanda jama’a ke fatan gwamnati ta yi a sabuwar shekarar ta 2024 mai kamawa.
Juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023 na kan gaba a jerin muhimman abubuwan da suka wakana a Nijar a tsawon shekarar 2023 musamman kasancewar abin ya faru ne cikin wani yanayin bazata wato a dai dai lokacin da kasar ke shan yabo daga kasashen duniya sakamakon lura da alamomin dorewar dimokradiya.
Kwamandan Rundunar Dogarawan Fadar Shugaban Kasa, Janar Abdourahamane Tiani ne ya jagorancin juyin mulkin, kafin daga bisani ya sami hadin kan shugabanin rundunar mayakan kasar ta Nijar inda suka kafa Majalissar Ceton Kasa ta CNSP.
Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika mambobin CEDEAO da UEMOA sun kira taron gaugawa a ranar 30 ga watan Yuli a Abuja wanda a karshensa suka yi Allah wadai da juyin mulkin sannan suka kakaba wa Nijar jerin takunkumi ciki har da rufe iyakoki da katse wutar lantarki da kamuwar kudade da kadarorin kasar a bankin bankuna na BCEAO sannan suka bukaci a mayar da Shugaba Bazoum kan kujerarsa kokuma ECOWAS ta yi amfani da karfin soja, lamarin da ya haddasa takun tsaka tsakanin kungiyar da sojojin juyin mulkin na Nijer wanda har ma ya shafi hulda da manyan kasashen duniya.
A sanarwar farko da suka bayar, sojoji sun ayyana matsalolin tsaro a sahun gaban dalilan kifar da gwamnati .
Darewar sojojin CNSP a kan karaga ta bada damar korar Jakadan Faransa haka kuma aka tilasta mata kwashe sojojin da ta girke a Nijar shekara da shekaru da sunan yaki da ta’addanci yayin da aka kori jakadiyar MDD bayan da aka rufe wa tawwagar gwamntin rikon kwaryar Nijar kofar taron MDD na shekara shekara kamar yadda dangantaka ta yi tsami a tsakanin kasar da makwafta matsalar da kwararru ke ganin wajibi ne hukumomin mulkin soja su gaggauta magancewa.
Haka shi ma mai fashin baki kan sha’anin tsaro ke da irin wannan tunani saboda haka ya shawarci hukumomin mulkin soja su bi dukkan hanyoyin da zasu taimaka Nijar ta fita daga halin kadaicin da ta tsinci kanta ciki.
Daukan matakan yaki da tsadar rayuwar da ta samo tushe daga takunkumin CEDEAO wani bangare ne na abubuwan da ‘yan kasa ke fatan majalissar CNSP ta bai wa kulawar musamman a shekarar nan ta 2024 ba’idin sauran bukatun da suka shafi ci gaban al’umma wace ke jiran ganin yaki da cin hanci.