A daren talatar nan ne babban Atoni kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano Barrister Haruna Isa Dederi ya fitar da wasu shafuka na kudin daftarin shari’ar wadda ke nuna gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ne yayi nasara a shari’ar da kotun daukaka karar ta yanke a ranar Juma’ar data gabata, sabanin yadda alkalan ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda kotun ta jaddada nasarar daya samu a kotun kararrakin zabe ta Kano.
Al’amarin dai ya haifar da cece kuce a tsakanin al’umar jihar Kano, musamman ‘yan siyasa da masana harkokin demokaradiyya da kuma lauyoyi. Barr Garba Abubakar wani lauya mai zaman kansa a jihar Jigawa yace “Abin da ya fi tasiri shine hukuncin da aka karanta a zauren kotu fiye da abin da wannan abu daya fita daga baya. Masana sunyi hashen irin wannan yanayi ka iya faruwa sanadiyyar kuskuren alkalami ko keken buga rubutu, don haka aka baiwa alkali dama ya dawo kotu ta gyara wannan kuskure. Sai dai yace abin takaici ne ace wannan kuskure ya fito daga Kotu, la’akari da yadda shari’ar ta dauki hankalin ‘yan Najeriya.”
Ana sa bangaren, Barrister Ibrahim Chedi sakataren kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Kano yace, “Abin lura a nan shine ga wanda ya karanta daftarin hukuncin baki dayan sa zai fahimci cewa, nasarar dake cikin hukunci ta Jam’iyyar APC ce, kuma idan aka tashi ba’a karanta wani bangare na hukunci a bar wani. Abin daya kamata shine Jam’iyyar NNPP ta mayar da hankali akan batun daukaka kara zuwa kotun koli kawai.”
Su kuwa, masu Nazari akan kimiyyar siyasa da kuma lamuran demikaradiyya na ganin al’amarin ya dumama yanayin siyasa a Najeriya baya ga dumamar yanayin siyasar Kano. Dr Kabiru Sa’idu Sufi malamin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano. “Yace babu mamaki wannan lamari ya sanya hakalin ‘yan kasa baki daya ya sake komawa kan hukuncin da ita kotun koli zata yanke akan batun.”
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, mahukunta a kotun daukaka karar ta Abuja data yanke wannan hukunci ba su fito sun tabbatar da sahincin waccan takarda dake bada nasara Abba Kabiru Yusuf ba ko akasin haka.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5