Yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben Gwamnan jihar Kogin Nigeria da aka gudanar jiya Asabar, jam’iyyun siyasa a jihar Kogin sun mai da martani a kan matakin da Hukamar ta INEC ta dauka na soke zaben wasu mazabu daga wasu kananan hukumomi dake fadin jihar Kogin.
Kakakin Hukumar ta INEC a jihar Kogin, Alhaji Halliru Haruna, ya yi karin haske cewa zargin tafka magudi a mazabu 9 dake kananan hukumomin Manongo, Ajakuta, da kuma karamar hukumar Okene wato mahaifar Gwamna Yahaya Bello yasa suka soke zaben.
Jam’iyyar adawa ta SDP wadda Hon. Murtala Ajaka yake yiwa takara ta ce ta yi maaraba da wannan mataki na hukumar zaben na soke zaben wadannan yankuna. Hon. Dalladi Bababudon shine Shugaban SDP a yankin Lokoja, ya ce sun ga kurakurai da dama ciki har da fitar sakamakon wasu runfunan zabe tun kafin yin zaben.
Ya kara da cewa duk kokarin da suka yi domin a nuna musu takardan sakamakon zaqbe na ainihi amma hakar su bata cimma ruwa, a don haka yana gani matakin soke zabe a wasu wurare ya dace.
To Amma ana ta gefen, jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kogin ta ce wannan sharri ne kawai aka kulla mata. Alhaji Maikudi Bature Shugaban APC a Lokoja ya ce duk da yake akwai lauje cikin nadi za su ci gaba da bin doka.
Kawowa lokacin hada wannan rahoto dai hukumar zaben jihar Kogin ta fara bayyana sakamakon wasu kananan hukumomi yayin da ake sa ran kammalawa zuwa bayan La’asariyar Lahadin nan ko kuma zuwa cikin dare.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da rahoto cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5