A Karon Farko A Tarihin Amurka An Tsige Kakakin Majalisar Wakilai

Kevin McCathy

'Yan majalisar dokokin Amurka sun kada kuri'ar tsige kakakin Majalisar Wakilai daga mukaminsa, wannan shi ne karon farko da aka taba ganin haka a tarihin Amurka.

WASHING, D. C. - Majalisar Wakilan Amurka ta bude wani sabon babi bayan da kokarin wasu masu ra’ayin rikau na tsige ‘dan jam'iyyarsu ta Republican Kevin McCarthy daga mukamin kakakin majalisar ya yi nasara tare da goyon bayan 'yan Democrat.

A jiya Talata aka zartar da kudurin da ‘Dan majalisar Wakilai Matt Gaetz daga jihar Florida ya gabatar, tare da goyon bayan 'yan Republican takwas da duk 'yan Democrat da suka halarci zaman jefa kuri'ar. Matakin ya sa McCarthy zama kakakin majalisa na farko a tarihin Amurka da aka tsige daga mukaminsa, wani wulakanci mai zafi da ya fuskanta bayan kwashe kasa da watanni tara yana rike da mukamin.

Kevin McCarthy, na California - Capitol , Washington, Oct. 3, 2023.

‘Dan jam'iyyar na Republican daga jihar California ya fada a wani taro da yayi jim kadan bayan tsige shi cewa ba zai sake neman mukamin ba. Wannan dai wani abu ne da ya ba ‘yan majalisa daga bangarorin jam’iyyun biyu mamaki sosai ya kuma sa su tunanin abin da gaba zata haifar.

Matt Gaetz - US Capitol , Washington, Oct. 2, 2023.

‘Dan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Republican Patrick McHenry, wanda yanzu shi ne mukaddashin kakakin Majalisar, ya ayyana cewa majalisar ta je hutu har sai bangarorin biyu su yanke shawara kan neman mafita. Ga dukkan alamu dai yanzu babu wani da zai maye gurbin shugabancin ‘yan Republican masu rinjaye a majalisar wakilan yanzu da McCarthy ya ce ba zai sake tsayawa takara ba.

-AP