Amma kwararu na ganin an fara daukar matakan gyara ne.
Kungiyar Koli ta a'ladun Kabilar Igbo wacce aka fi sani da OHANEZE N'DIGBO ta yi Allah wadai da matakin dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele, tare da bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka a matsayin wata alama ta nuna wa Kabilar Igbo wariyar jinsi.
Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da darektan Kula da Sha'anin Kasa na Kungiyar, Mazi Chima Uzor ya raba wa manema labarai.
Uzor ya ce ba a bi ka'ida wajen dakatar da Emefiele ba, saboda haka Kungiyar ta na ganin mataki ne da aka yi da gangan, da nufin kawar da 'yan kabilar Igbo daga Ofisoshin Gwamnati. Amma Masanin harkokin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya aiyana matakin ne da cewa idan kida ya canja dole rawa ta canja.
Mikati ya ce masu binciken abubuwa da ke kai komo a Babban Bankin Najeriya sun nuna cewa an yi abubuwan da ba daidai ba ne a zamanin mulkin Godwin Emefiele, inda ya ce an bada basussuka na tallafin noma amma wadanda aka ba bashin ba su mori tallafin ba, saboda an bi ta baya ana karbai wani kaso akan kudin. Mikati ya ce haka aka yi ta yi da batun canjin dala, kawai sai a ba mutun dalar Amurka dayawa ba tare da yayi aikin komi ba, kawai sai a ce masa ga inda zai tafi ya canja dalar a kasuwar bayan fage, kawai saboda ana so a azurta mutum domin ya san Gwamnan Babban Bankin Najeriya. Mikati ya ce idan aka samu Shugaba da yake da tausayin talakawa a kasar, barin irin wanna almundahana ba zai yiwu ba.
Shi ma Masanin tattalin arziki kuma mai nazari a harkar Kudi,Yusha'u Aliyu ya ce cire Emefiele yana da nasaba ne da zarge zarge da aka yi ta yi a game da abubuwan da suka rika wakana a CBN ba tare da bin ka'ida ba.
Yusha'u ya ce Hukumar tsaro ta kasa ta ce ta kama shi ne domin ta yi bincike akan wasu tsare tsare da ya kawo a kasa, musamman ma sauyin kudi da aka yi a baya bayan nan da bai samu nasara ba. Yasha'u ya ce idan za a yi bincike irin wannan to dama cire mutum ake yi a mukamin sa.
Shi kuwa tsohon Sanata wanda ya wakilci Katsina ta Arewa, Ahmed Babba Kaita ya yi tokaci cewa wannan mataki da Gwamnatin Tinubu ta dauka, abu ne da zai kawo wa kasa nasara. Babba Kaita ya ce kar a tsaya akan Emefiele kawai, a kai binciken har kan 'yan Kabal da wasu wadanda suke kusa da tsohon shugaban Kasa Mohammadu Buhari. Babba Kaita ya ce idan har binciken da za ayi zai fadada zuwa dukannin ma'aikatun Gwamnati, to shi yana goyon bayan Bola Ahmed Tinubu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya Peter Afunanya ya fitar a yau, ta na cewa hukumar za ta nemi umurnin kotu domin ci gaba da tsare Emefiele har tsawon lokacin da za a yi masa tambayoyi.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5