Bayan kona motocin dakon albasa da 'yan ta'addan yankin ke yi an kuma samu asarar rayukan direbobi da yaransu, dalili kenan suka yi kiran hukumomin kasashen Sahel su dubi wannan matsala da idon basira.
Wani matukin babbar mota da ke dakon albasa daga Nijer zuwa kasashen Cote d’Ivoire da Ghana, ya ce tsakanin Laraba da Alhamis ‘yan ta’adda sun kona motocin dakon albasa sama da 10.
A bidiyon da ya nada akan hanyarsu ta dawowa gida, ana ganin gawarwakin wasu manyan motocin Tirela da suka kone kurmus a bakin hanya a wani jejin Burkina Faso wanda ke daya daga cikin yankuna mafi hadari a kasar mai fama da matsalolin tsaro, inda a ‘yan makonin nan ‘yan ta’adda suka bullo da salon kona motocin matafiya .
A wannan karon abin ya rutsa da tirelolin albasa sama da 10 mallakar ‘yan Nijar, lamarin da ya tada hankalin shugabannin kungiyoyin manoma da masu kasuwancin albasa irinsu Alhaji Moustapha Kadri sarkin Abzin.
Ko da yake a wannan karon mutanen da suka aikata wannan danyen aiki ba su taba direbobi da yaransu ba, gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jigila ta UTTAN, a ta bakin kakakinta Gamatche Mahamadou, na cewa yanayin da ake ciki a tsakanin Nijar da kasashe makwafta irinsu Burkina Faso da Mali masu fama da mamayar mayakan jihadi abu ne da ke barazanar jefa drebobi zaman kashe wando.
Ganin yadda matsalar ta fara ta’azzara ya sa manoman albasa da masu motocin dakon albasar zuwa kasuwannin kasashen waje suka soma wadanan kiraye-kiraye.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan ta’addan yankin Sahel da barayin kan hanya ke afka wa matafiya akan hanyoyin da ke tsakanin Nijar, da Burkina Faso, da Mali ba, inda suke kona motoci wani zubin har da ma lodin fasinja ko na kayan da suke dauke da su.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5