Mahalarta taron da gwamnatin jamhuriyar Nijer ta shirya da hadin gwiwar masu hannu da shuni a birnin Paris da nufin tattara kudaden gudanar aiyukan ci gaba da inganta rayuwar al’umma, sun yi alkwarin bada kudaden da suka haura bilion 45 na euro don daukan dawainiyar tsarin ajandar da ake kira PDES a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026.
Kusan dukkan wasu hukumomi da kungiyoyin da ke fada a ji a duniya ne suka hallara a wannan taron da Nijer ta shirya a Paris da hadin gwiwar Bankin Duniya da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Tarayyar Turai.
Gwamnatin Faransa da kungiyoyi masu hannu da shuni sun yi nazarin tsarin da Nijer bayyana a matsayin shirin aiyukan ci gaba da inganta rayuwar al’umma PDES na shekarar 2022 zuwa 2026.
Shugaba Mohamed Bazoum ne ya gabatar da tsarin da zummar jan ra’ayin gwamnatoci da manyan ‘yan kasuwa don ganin sun raka kasar a wannan tafiya ta tsawon shekaru 4.
Shugaban ya ce tsarin na PDES a wannan karon mun yi masa taken dake cewa, Nijer kasa mai kyaukyawan tarben baki da bada damar zuba hannun jari.
Ya kuma kara da cewa an tsara fasalin aiyukan na PDES da shawarwarin dukkan rukunonin al’ummar Nijer, tare da la’akari da ka’idodin kasa da kasa. Wannan tsari abu ne da ke fayyace mahimman aiyukan da gwamnatin kasar ta sa gaba a fannonin da suka hada da aiyukan ci gaba da inganta rayuwar al’umma ta hanyar raya al’adu da kare muhalli.
Gamsuwa da abubuwan da suka ji a yayin wannan zama ya sa masu hannu da shuni yin na’am da bukatun hukumomin na Nijer, tare da yin alkawalin bayar da biliyan 45 na euro wato fiye da abind a aka yi hasashe tun farko.
Shugaban kungiyar farar hula ta MOJEN Siradji Issa wanda ya halarci wannan taro, ya alakanta yunkurin na masu hannu da shuni da yanayin tafiyar mulkin Nijer a yau.
Sai dai a na sa ra’ayin Salissou Amadou wani jigo a kungiyar Sauvons le Niger, ya nuna dari dari a game da makomar wannan tsari hasalima ya na mai kallon abin tamkar zacen ‘yan matan amarya a bisa la’akari da yanayin da aka tafiyar da irin wannan tsari a tsakanin 2017 da 2022.
Shugaban kasa ya kudiri aniyar rage talauci daga kashi 43 daga cikin 100 a halin yanzu zuwa kashi 35 a shekarar 2026 ta hanyar tsarin na PDES, inda gwamnatinsa za ta karfafa aiyukan noma da kiwo fannin ma’adanai da man fetur.
Kashi 45 daga cikin kudaden aiwatar da wannan tsari Nijer za ta dauki nauyinsu.
Saurari rahotan cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5