Gasar Kwallon Kafar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai

  • Murtala Sanyinna

Gasar Kwallon Kafar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai

An tsara jadawalin fafatawa a zagaye na 2 na gasar kwallon kafar cin kofin zakarun nahiyar turai, bayan kammala zagayen rukuni-rukuni.

Kungiyoyi 16 ne dai suka sami tsallakewa a matsayin na daya da na 2 daga kowane rukunin gasar, wadanda kuma aka hada su da junan da za su fafata a wani biki da aka gudanar jiya Litinin a Istanbul, babban birnin kasar Turkiyya.

Hadin da ya fi jan hankalin masoyan kwallon kafa shi ne na Real Madrid ta kasar Spain da Liverpool ta Ingila, wadda za ta maimaita karawarsu a wasannin karshe na gasar na shekarar da ta gabata ta 2021.

Haka kuma za’a maimaita karawar wasar karshe ta gasar ta 2020 tsakanin PSG ta kasar Faransa da Bayern Munich ta kasar Jamus.

Manchester City za su kara da RB Leipzig, Chelsea ta fafata da Borussia Dortmund ta kasar Jamus, inda Tottenham kuma za hadu da AC Milan ta kasar Italiya.

A Italiya din kuma Inter Milan zata kece raini da FC Porto, Napoli zata barje gumi da Eintracht Frankfurt, yayin da Benfica kuma zata fafata da Club Brugge ta kasar Belgium.

Za’a buga wasanni farko ne a ranakun 14 zuwa 15 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa, yayin da wasanni na 2 kuma za su zo a ranakun 21-22 ga watan Maris.

A daya bangaren kuma an shata jadawalin fafata wasannin yada kanin wani na gasar Europa League, inda za’a yi karon battar karfe tsakanin Barcelona da Manchester United.

A sauran wasannin na Europa kuma Juventus zata kara da Nantes, Sporting Lisbon da Midtjy-land, sai Shakhtar da Rennes, Ajax ta buga da Union Berlin.

Bayer Liverkusen zata kara da Monaco, Sevilla da Eind-hoven, yayin da FC Salzburg zata kece raini da AS Roma.

Kungiyar kwallon kafar Southampton ta ba da sanarwar sallamar mai horar da ‘yan wasanta, Ralph Hasenhuttl, sakamakon koma bayan da take fuskanta a wasanni.

Sanarwar korar kocin ta zo ne kwana daya bayan kashin da kungiyar ta sha a hannun Newcastle a wasan gasar Premier a karshen mako.

Wannan ne kuma ya ba da adadin wasanni 8 na gasar da kungiyar ta Southampton ta sha kashi a cikin wasanni 14 a wannan kakar wasanni a karkashin kocin.

Hasenhuttl ya koma kungiyar ta Southampton ne a shekara ta 2018, inda ya kwashe tsawon shekaru 4 yana aikin, to amma kuma kungiyar ta sha fama da koma baya na rashin nasara a wasanni tun somawar kakar wasanni ta bana.

A Ingila din kuma, mai horar da ‘yan wasan kungiyar Tottenham, Antonio Conte, yayi barazanar barin kungiyar muddin magoya bayan kungiyar ba sa nuna goyon baya gareshi da kuma kungiyar.

Kungiyar ta Tottenham dai ta soma kakar wasanni ta bana ne da karfin gaske, kafin daga bisani ta dan fuskanci matsalolin rashin samun nasara.

A baya-bayan nan Liverpool ta bi ta har gida ta doke ta da ci 2-1 a wasan gasar Premier a jiya Lahadi, lamarin da ya kara tunzura magoya bayan kungiyar suka soma yin kakkausan suka ga kocin da kuma ‘yan wasan, inda wasu suke kira da a sauya kocin, saboda zargin rashin ingantaccen tsarin horarwa.

Lamarin kuma ya bata wa Conte rai, musamman sa’adda ‘yan kallo suka yi masa sowa a filin wasa, inda ya ce muddin ba’a sami sauyi ba, to kuwa zai iya barin kungiyar.

Saurari shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gasar Kwallon Kafar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai