Wata kotu a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta yankewa Sanata Peter Nwaoboshi hukuncin zaman gidan yari har tsawon shekara bakwai akan halalta kudaden haram.
Nwaoboshi, shi ne sanatan da ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jam'iyyar APC mai mulki.
Kotun to yanke hukuncin ne a ranar Juma’a bayan da ta sami Nwaoboshi da laifin damfara da halalta kudaden haram tare da wasu kamfanoninsa guda biyu.
Kotun ta kuma yanke hukuncin a rufe kamfanonin biyu masu suna Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd kamar yadda doka ta tanada.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta bayyana wannan hukunci a shafinta na Facebook a ranar Juma’a.
EFCC, wacce ita shigar da karar, ta kalubalanci wani hukunci da wata babbar kotu ta yanke karkashin alkalancin Mai Shari’a Chukwujeka Aneke a ranar 18 ga watan Yunin 2022, inda aka wanke Nwaoboshi daga tuhume-tuhumen da ake masa da kamfanoninsa.
Sai dai kotun ta Legas wacce Mai Shari’a Abdullahi Bayero da Obande Ogbuniya da Peter Affen suke alkalanci, ta ce hukuncin Aneke akwai kurakurai a ciki, saboda masu shigar da kara sun bayyana kwararan hujjoji da suka nuna Nwaoboshi na da laifi.
Ita dai hukumar ta EFCC ta shigar da kara akan wani gida da aka saya mai suna Guinea House da ke layin Marine Road a Apapa akan kudi naira miliyan 805.
Daga cikin kudin an biya mai sayar da gidan naira miliyan 322, wanda kamfanin Suiming Electrical Ltd ya biya da sunan Sanata Nwaoboshi da kamfanin Golden Touch Construction, kudande da aka gano cewa daga cikin wadanda aka samo ne ta hanyar damfarar.