Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kasar Andalus bayan da takwaran aikinsa Pedro Sanchez ya gayyaci ce Birnin Madrid.
Yayin ziyarar, Buhari zai kuma gana da Mai Girma Sarki Felipe na shida a wani taro da za su yi na daban.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar da sa hannun kakakin Buhari, Femi Adesina, ta nuna cewa shugaban na Najeriya zai tattauna da shugabannin biyu kan batutuwan da suka shafi muradin kasashen biyu.
“Hakan kamar yadda ake tsammani, zai kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan batutuwan da dama da suka shafi kasashen biyu.” Adesina ya ce.
Batutuwan za su hada da, mika maido da mutanen da aka samu da aikata laifi, al’adun Gargajiya, hadin kai wajen yaki da manyan laifuka da bunkasa harkokin tsaro da sauransu.
Kazalika kasashen za su hada kai a bangarorin samar da makamashi, kasuwanci, saka hannun jari, sufuri, kiwon lafiya da kuma wasanni a cewar fadar shugaban Najeriya.
Daga cikin manyan jami’an gwamnatin Najeriya da za su rufawa Buhari baya, akwai Ministan harkokin wajen Geoffrey Onyeama, Babban Atoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Ministan masana’antu da saka hannun jari Otunba Adeniyi Adebayo, Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed da Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.