ABUJA, NIGERIA - Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta ce ta na bukatar aiki tare da rundunar tsaron sirri ta cikin kasa DSS ga lamuran aikin hukumar don bin ka’ida.
Shugaban hukumar alhazan Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana bukatar a ziyarar da ya jagoranci tawaga zuwa ofishin daraktan DSS a Abuja Yusuf Bichi.
Kunle Hassan ya ce DSS za ta taimaka ainun wajen cigaba da tantance masu niyyar umrah da kuma aikin hajji don hana duk mai mummunar dabi’a zullewa ya shiga kasa mai tsarki.
Hakanan Hassan ya bukaci hukumar ta sanya baki wajen fidda sunan Najeriya daga jerin kasashen da ta dakatar da shigar su kasar ta don nau’in annobar korona na OMICRON.
A jawabin sa, shugaban na DSS Yusuf Bichi ya ba da tabbacin cigaba da aiki da NAHCON don gudanar lamura bisa tsari.
Hakanan Bichi ya amince da zai yi magana da hukumomin Saudiyya don janye hana jiragen Najeriya sauka kai tsaye a Saudiyya.
Daidai kammala rubuta wannan labari mu ka samu labarin Saudiyya ta dage wannan dakatarwar ta hana shiga kai tsaye kasar ta ga kasashe ciki da Najeriya.
Sabon matakin janye takaita hada-hada don korona da Saudiyya ta yi zai ba da kwarin guiwar yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana.