A daidai lokacin da Musulmi a fadin duniya ke gudanar da azumin Ramadana cikin yanayi da ba a taba gani ba sanadiyar annobar coronavirus, an rufe wuraren ibadu da sauran mu’amaloli na yau da kullum a kasashe da dama.
Magajin garin birnin Laurel dake jihar Maryland a Amurka, Craig A. Moe, ya jagoranci rabawa Musulmai abinci a masallacin cibiyar harkokin addinin Musulunci - Islamic Community Center Lauren ICCL, domin ragewa mutane radadin coronavirus.
Moe ya yabawa shugabannin cibiyar ta ICCL kan irin rawar da suke takawa wajen samar da tallafi ga mabukata a wannan lokaci na COVID-19. Ya kuma fadawa ma’aikaciyar VOA Hausa cewa, wannan ba shi ne tallafi na farko da masallacin ya bai wa jama’a a Laurel ba.
Shekara guda kenan da shugaban hukumar gudanarwa ta masallaci, Syed Osama Hasan, ya fara rabon abinci ga al’umma a irin wannan lokaci na Ramadana da hadin gwiwar ofishin Magajin garin birnin.
Syed ya ce ba abinci kawai suke tallafawa mutane da shi ba, su na da wani tsari da suke taimakawa mabukata da kudade domin bin ka’idodin musulunci.
Kasancewar annobar COVID-19 ta sa an dakatar da zuwa wuraren ibada, cibiyar ta ICCL ta bullo da wani sabon shiri na gayyatar mutune zuwa karbar abinci, amma babu wani da zai fito daga motarsa. Za su karba ta kofa guda, su fita ta wata kofar.
Masu rabon abincin dai sun bai wa kansu tazara kamar yadda hukumomi suka bayar da shawara. Magajin gari Moe da shugabannin masallacin ne da farko suke fara gaishe da mutum idan ya shiga harabar da motarsa domin ya karbi abinci da ruwan sha.
Daga karshe an bayar da kwanukan abinci 350, kuma Syed ya ce ko wacce ranar Asabar ta wannan wata na Ramadana za ayi rabon abinci.