Tsohon jarumin masana’antar fina-finai ta Bollywood Irfan Khan, wanda yayi fice a duniya kan rawar da ya taka a fina-finan “Slumdog Millionaire” da Life of Pi” ya mutu yana da shekaru 54 a duniya.
Mai Magana da yawunsa ya ce, Khan ya mutu yau Laraba a Asibin Mumbai, inda aka kwantar da shi tun farkon wannan makon kan wata cuta da ta shafi babban hanjin cikinsa. An dai yiwa Khan aiki a Birtaniya bayan da aka gano yana da wata nau’in cutar daji a shekarar 2018.
Shi dai dan asalin Rajasthan ne dake yammacin India, ya kuma shiga harkar shirya fina-finai a shekarar alif 988 inda ya fara da wasan drama na “salaam Bombay.” Khan ya zamanto tauraron jarimi a fitattun fina-finan Bollywood, ciki har da “The Namesake” da “The Lunchbox” da kuma “Paan Singh Tomar” wadanda suka sa ya samu lambar yabo ta India, wato fitaccen jarumi na shekarar 2012.