Jami’an Tsaro Sun Dukufa Wajen Yakar Rikicin Makiyaya Da Manona A Jihohin Adamawa Da Taraba

Rikicin makiyaya da manoma a Adamawa

Rundunonin tsaro a arewa maso gabas irin su sojoji, ‘yan sanda, da jami’an tsaron farin kaya Civil Defense sun hada kai wajen yakar rikicin makiyaya da manoma

Kwamandan rundumar sojin Nigeria ta 23 dake Yola Birgediya Bello Muhammad y ace sun aikin atisayi na “Operation Show of Force” da zummar kafa mayaka na musamman da suka kunshi sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya ko Civil Defense domin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihohin Adamawa da Taraba.

Kwamandan y ace tuni kwaliya ta fara biyan kudin sabulu saboda haka za su ci gaba da hadin kan da suka samu tsakaninsu da sauran jami’an tsaro dalilin sabon yunkurin.

Y ace a kowane yaki da su keyi a yankin arewa maso gabas suna yi tare ne. ‘Yan sand aba su fita su kadai haka ma sojoji ko NDLEA bas u fita su kadai.

Rayuka da dama sun salwanta sanadiyar rikicin baya ga al’ummomin da aka raba da muhallansu da dimbin dukiyoyinsu.

Suleiman Baba kakakin rundunar garin kaya ta Civil Defense a jihar Adamawa ya ce hukumomin tsaro suna yin aiki kafada da kafada tare da sarakunan gargajiya saboda galibi su ne suke da alhakin ba da gonakin noma. Idan aka fitar da wuraren kiwo da na noma farkon damuna.

A saurari karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Tsaro Sun Hada Gwuiwa Wajen Yakar Rikicin Makiyaya Da Manona A Jihohin Adamawa Da Taraba