Dubban jama’a ne rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. haka kuma daruruwan wadanda suka koma garuruwansu yanzu haka sun rasa katunan zaben su.
Wannan na zuwa ne a yayinda hukumar zaben Najeriya ta INEC, ta bada zuwa karshen wannan watan na Agusta a matsayin lokacin dakatar da aikin sabunta katin zaben a kasar. Al’ummomin yankunan sun yi korafi ga hukumar INEC, akan cewa ta yiwa Allah ta dube su da idon rahama wajen samar musu katunan zabe kafin karshen wa’adin.
Mr. Adamu Kamale, dan majalisar wakilai dake wakiltar yankunan Madagali da Michika, ya tabbatar da cewa yanzu haka akwai daruruwan jama’a da basu da katunan zabe, ga kuma lokaci na kurewa, lamarin da ka iya hana su gudanar da zabe.
Hukumar zaben INEC, a ta bakin Barista Kassim Gana Gaidam wanda shine kwamishinan hukumar a jihar Adamawa, ta bada tabbacin cewa za’a cigaba da aikin bada katunan a wadannan wuraren.
Yanzu haka 'yan siyasa, da kungiyoyi da ma shugabanin addini na cigaba da kiran jama’a akan su fito domin sabunta katinan su.
Suleiman MD Numan, wani matashin dan siyasa ya bayyana katin zaben a matsayin makamin kawo sauyi, ba wai fitina ba.
Ga karin bayani a cikin sauti daga Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum