Kamfanonin Jiragen Sama Ba Zasu Bari A Safarar Yaran Da Trump Ya Raba Da Iyayensu Da Jiragensu Ba

Jirgin saman kamfanin American

Wasu kamfaanonin jiragen sama na Amurka sun lashi takobin hana jami'an gwamnatin kasar safarar yaran da aka raba da iyayensu da jiragensu ba saboda matakin gwamnatin ya sabawa abubuwan da suke darajawa

To gabanin faruwar hakan, matakin da shugaba Trump ya dauka na raba iyaye da ‘ya’yan nasu, ya sa wasu kamfanonin jiragen sama na Amurka suka nemi gwamnatin kasar da kada ta yi amfani da jiragensu wajen safarar jami’anta da ke rakiyar yaran bakin haure da aka raba da iyayensu a kan iyakar Amurka da Mexico.

Kamfanin jiragen American da United da na Frontier, duk sun nuna aniyarsu ta kin yin safarar jami’an kula da shige da fice a karkashin wani kwantiragi da suka yi da gwamnati.

A wata sanarawa da kamfanin American Airline ya fitar, ya ce matakin raba ‘ya’ya da iyayensu, “ya sabawa abubuwan da kamfanin yake darajawa.”

Wani ma’aikacin jirgin sama, Hunt Palmquist, ya rubuta a jaridar Houston Chronicle cewa, sau biyi ana jigilar jami’an shige da fice tare da yaran da suke yiwa rakiya zuwa wani kebabban wuri da aka ware musu.

Amma ya ce bayan da ya gane abin da yake faruwa, sai ma’aikacin ya sha alwashin zai fice daga jirgin idan har yaga za a sake jigilar yaran, “saboda wannan mataki da gwamnati ta dauka tare da hadin kan kamfanin da yake aiki, mataki ne na nuna rashin sanin ya kamata.”

Ita dai hukumar tsaron cikin gida ta Homeland Security ta kwatanta matakin da kamfanonin jiragen suka dauka na kin jigilar yaran a matsayin abin takaici.