Sharudda Don Cin Jarabawar Ganawar Daukan Aiki “Interview”

Akwai abubuwa muhimmai da ya kamata mutane su ba kulawa ta musamman, Sau da yawa mutane basa lura da yadda suke gaisawa da mutane wajen bada hannu.

Da yawa rashin iya gaisawa da mutane kan sa mutun ya rasa aikin shi, ko kuma ya saka mutun cikin wani hali. Masana halayyar dan’adam sun bayyana wani rahoto da ya jaddada muhimancin mutane su rika lura da yadda suke gaisawa da mutane.

Domin kowane irin mutun da irin yadda ake gaida shi, yadda mutun zai gaisa da abokin sa ya banbanta da yadda zai gaisa da mutane a lokacin da aka gayyace shi ganawar daukar aiki “Interview” haka da yadda mutun zai gaida shugaban sa a wajen aiki.

Da yawa mutane kan mika hannu ba tare da nuna wata alama ta girmamawa ba, ko kuma mutun ya gaisa da mutun yana murda hannun mutun da dai wasu abubuwa da basu kamata mutun yayi ba, wanda hakan yana iya bayyana ma mutane wasu abubuwa dangane da kai.

Don haka yake da muhimanci idan mutun zai gaisa da mutane yasan suwa yake gaisawa da su don gujema abun magana. Haka kada mutun ya gaisa da mutane ya rike musu hannu da ya wuce na tsawon dakika biyu zuwa uku.

Akwai bukatar mutun ya rike hannun mutane da muhimanci da karfi ba tare da matse hannun ba, hakan yana nuna ma mutun cewar wannan mutumin yana da kuzari da azama koda an dauke shi aiki zai iya gabatar da aikin sa batare da ragwanci ba.