Wata Mata A China Ta Bi Jakarta Cikin Na'urar Binciken Kwakwab

Na'urar Binciken Kwakwab

Mutane da suka damu da yadda ake masu sace-sace a tashoshin jiragen sama ko na kasa, a dalilin bincike da akanyi don magance matsalar tsaro, wata matashiya a kasar China ta magance wannan matsalar da sabon salo.

Ma’aikatan tashar jiragen kasa ta ‘Dongguan Railway’ a kudancin kasar China, sunga abun mamaki, a dai-dai lokacin da wata matashiya ta isa tashar don tafiya zuwa hutu, an bukaci ta saka Jakunkunanta cikin na'ura mai duba kayan mutane, da zummar tantance abubuwan dake cikin jakar.

Matashiyar bata yadda ta tura Jakarta batare da ta san abun da za’a yima jakar tataba, a dai-dai lokacin da jakar take wucewa cikin na’urar, ta yanke shawarar tabi jakartata.

Koda ma’aikatan tashar suka duba sai suka ga mace tare da Jakarta, kwamfuta ta nuna matar a durkushe sanye da takalminta mai tsini, mahukunta sun bayyana cewar basu da masaniyar dalilin da yasa matar taki amincewa ta tura jakar cikin na'urar binciken kwakwab.

Amma ana tunanin cewar matar na dauke da kudade ne a cikin jakar, wanda bisa ga al’ada a kasar ta China mutane kan dauki makudan kudade a lokacin tafiya zuwa hutu.

A lokacin da aka shaida ma matashiyar cewar duk jakunkunanta sai sunbi ta cikin na’urar, sai ta yanke shawarar itama tabi don ta tabbatar da tsaro ga jakartata. Hakan ya jawo hankalin mahukunta, domin kuwa wannan wani bakon al’amari ne.