Wani matashi Joel Ifill, wanda ya kirkiri jirgi sama mara matuki watau ‘Drone’ wanda za’a iya yarwa, bayan anyi amfani da shi sau daya. Ya kirkiri jirgin ne don amfani da shi a yayin da ake da wata bukatar gaggawa, kana a yanayin da ke da rintsi.
Shi dai jirgin an kirkire shine da wasu sinadarai da suka hada da kwali, wasu karafa, wanda a duk lokacin da ya isar da sako ba za’a sake bukatar shiba.
Jirgin na iya daukar magunguna, ko kayan abinci da nauyin su ya kai kilo 20, matashin da ya kirkiri jirgin wanda mazaunin jihar California ta Amurka, ne ya bayyana dalilan da suka bashi kwarin gwiwa wajen kirkirar jirgin.
Yace ya lura a duk lokacin da akace akwai wasu kauyuka da ake bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa, basu isa cikin lokaci, musamman a kasashe masu tasowa, shi yasa ya fito da hanyar da zai bada tashi gudunmawa wajen tallafawa rayuwar mutane.
Domin kuwa jirgin baya bukatar kudade masu yawa wajen kera shi, kana ana iya amfani da shi cikin sauki da saukin kudin siya, tsarin jirgin shine ya shiga inda babu wani mahaluki zai shiga a lokacin tsanani.
Facebook Forum