Kamfanin sada zumunta na Twitter ya jaddada matsayarsa, da yake ba kowa da kowa damar fadan albarkacin bakinsa, biyo bayan kira da wasu mutane su ka yi, da cewar kamfanin ya rufe shafin shugaban kasar Amurka Donald J. Trump.
Kamfanin ya bayyanar da cewar babu dalilin da zai sa shi rufe shafin shugabannin kasashe a duniya, koda kuwa abin da suka rubuta na daukar hankali, da kawo takaddama mai zafi ne.
Wannan mataki na nufin zai ba mutane damar fadan albarkacin bakinsu, rufe shafin shugabanni ko boye wani rubutu da su ka yi a shafukansu, zai iya danne wasu bayanai masu matukar muhimmanci, da ya kamata a ce ‘yan kasa sun sani da kuma bayyanar da ra’ayin su akai.
Kamfanin na Twitter ya kara da cewa rufe shafin shugabanni zai iya haifar da rashin bai wa ‘yan kasa damar fadan albarkacin bakinsu da kuma bai wa su shugabannin shawara.
Shi dai shafin Twitter, wata dama ce da ta kan kawo ci gaba a duniya, da tattauna batutuwa masu nauyi.