Kasar Somalia Zata Dauki Wasan Kawance Na Kasa-Da-Kasa

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Somalia, ta bayyanar da cewar a shirye take ta dauki nauyin wasanin kasa-da-kasa, daga shekara 2018 mai suwa idan Allah ya kairai. Kungiyar ta kara da cewar a dalilin karuwar tsaro da aka samu a kasar a shirye take.

Shugaban kungiyar Abdiqani Said Arab, ya bayyanar da cewar lokaci yayi da ya kamata kasar Somalia ta karbi bakoncin wasanni, fillin wasan kwallon su zai iya daukar nauyin wasanni a shekarar 2018.

Saboda tsaro da aka samu a kasar, zamu iya daukar duk nauyin wasannin a kasar, domin al'ummar kasar ta Somalia, zasu bukaci kallon ‘yan wasan kasar su, a yayin da suke buga wasa a cikin kasar.

Ba kamar yadda suka dade suna yiba, na kallon ‘yan wasan kasar su, suna buga wasannin a wasu kasashen duniya, sabo da rashin tsaro a kasar tasu. Shugaban ya kara da cewar, zasu fara da gayyatar kasashen kudanci Afrika don gudanar da wasan kawance.