Facebook Zai Sanar Da Mutun A Duk Lokacin Da Aka Saka Hoton Shi

Kamfanin Facebook ya bayyanar da kudirin shi, na fito da wani sabon tsari, da a duk lokacin da aka saka hoton mutun a shafufukan yanar gizo, manhajar zata sanar da mutun cewar an saka hoton shi a wani guri. Da bayyana mishi wanda ya saka hoton.

Haka idan mutane sun ba kamfanin na Facebook damar ajiye samfurin fuskar su, a runbun ajiyar bayanai, wanda a duk lokacin da aka saka hoton su, na’ura mai kwakwalwa zata gane ta kuma sanar da mutun.

A cewar kamfanin, yana kokarin fitar da wannan sabon tsarin ne, don magance matsalar satar bayanan sirri na mutane, da wasu keyi wajen bude shafi da sunan mutun da hoton shi, wanda shafin yake na karya.

Tsarin ba zai fara aiki a kasar Canada da kasashen turai ba nan kusa, saboda tsarin dokokin bayanan sirri na mutane da suke da su, wanda suka sha banban da na sauran kasashe. Kamfanin dai na Facebook, na amfani da tsarin tantance fuskar mutun tun a shekarar 2010.

Yanzu haka kamfani zai kara inganta tsarin, don ba mutane damar kare kan su daga batagari masu bude shafufukan karya, da daukar bayanan mutane batare da izini ba.