Taron Bunkasa Kasuwancin Mata Na Duniya, Zai Gudana A Kasar India

Taron karama juna sani da bunkasa harkar kasuwanci, na duniya na kara karban matasa daga koina a fadin duniya. Taron dai ya hada da masu karamin karfi da masu sha’awar fara kowace irin sana’a. Taron da zai gudana a birnin Hyderabad a kasar India.

Taron mai take “Global Entrepreneurship Summit” da gwamnatin kasar Amurka ta shirya, zai samu halartar mai bama shugaban kasar Amurka shawara a harkar kasuwanci, kana ‘yar shugaban kasar Ivanka Trump, wanda zata hadu da Firaministan kasar Narendra Modi.

Taron da za’a gudanar na tsawon kwanaki uku, zai maida hankali akan mata ‘yan kasuwa. Kimanin mahalarta sama da dubu daya da dari biyar ne zasu samu zuwa daga kasashe dari da hamsin a fadin duniya. Za'a fara taron daga yau 28 zuwa 30 ga wannan watan.

Babu wani tabbacin cewar ko gwamnatin Trump, zata cigaba da gabatar da wannan taron a duk shekara, ganin cewar shugaba Obama, ya kaddamar da shirin a shekarar 2010.

Babban tunanin shugaba Trump, shine a maida hankali wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka. A watan Yuli dai ake sa ran Firaministan Indina zai gana da shuga Trump, inda ake tunanin zasu cinma matsaya don daukar nauyin cigaban shirin.