Yakamata jama’a su rungumi sauyin da zamani ya zo dashi masamman ma na rungumar irin matakan da mawaka ke dauka na ilimantar da jama’a akan cigaban da zamani ya zo dashi.
Wani matashin mawaki Ibrahim Ahmad Rufai, wanda ake kira da Home-boy, ne ya furta haka a wata zantawa da wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir.
Yana mai cewa mafi yawan wakokinsa na maida hankali ne wajen ilimantarwa kan yanayin zamantakewar tsakanin alumma tare da nusar da mutane muhimmancin zaman lafiya da son juna inji.
Ibrahim Home-boy ya ce mawaka irinsu kan fuskance kyama daga wajen mutane dangane da sana’ar da suka zaba wa kansu tare da kallon su a matsayin mutane da basu da da’a, bare har a kulla mu’amala da su a harkokin zamantakewa.
Ya ce ya fi maida hankali wajen yada manufar zaman lafiya da yadda jama’a zasu tafiyar da rayuwarsa, da zamani sanadiyar ganin yadda rayuwa ke da wuyar sha’ani a wannan lokaci.
Ya kara da cewa yana waka ne domin sha’awa da son fadakarwa , ko da yake ba da waka ya dogara ba, yana da wata sana’ar wadda ya dogara da ita.
Facebook Forum