Sani Sabo: Babu Wanda Yafi Wani Kwakwalwar Karatu, Sai Dai Kwazo

Sani Sambo

Sani Sabo, dan asalin karamar hukumar Kankia dake jihar Katsina, wanda ya samu nasarar kammala karatun firamari da sakandire duk a jihar su ta katsina.

Bayan ya kammala karatun shi na sakandire, ya samu sakamako mai kyau, hakan yasa ya cigaba da fadada karatun shi, zuwa mataki na gaba. Ya fara digirin farko a babbar jami’a ta tarayya dake jihar Sakkwato, Usman Danfodio.

Ya kammala karatun digiri a fannin (B.Sc. Applied Chemistry). Faduwa tazo dai-dai da zama, domin kuwa bayan kammala bautar kasa da yayi, sai ya samu aikin malanta a jamia’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina,

Hazakar Malan Sani, tasa bai yi kasa a gwiwa ba, ya cigaba da fadada karatun shi a jami’ar da yake aiki, a matakin digiri na biyu. Ya samu damar kammala digirin shi na biyu, a bangaren (In-Organic Chemistry).

Malan Sani, yayi nasarar lashe jarabawa da ake ma zakakurai da ke fannoni daban daban, a inda ya zamo matashi na farko da ya lashe jarabawar daga jihar ta Katsina. Hakan ya bashi damar fara karatun digirin digirgir a kasar Burtaniya.

Lura da irin wannan nasarar da malan Sani ya samu, babu shakka mutun ne mai kwazo kwarai da gaske da maida hankali. Tuni malan Sani, ke taka rawar gani wurin bada ta shi gudumuwa a kasar ta Najeriya, saboda malami ne na Jami’a. Ya kuma dau alwashin komawa kasar Najeriya, bayan ya kammala karatun shi a kasar Ingila

A cikin zantawar mu da malan Sani, ya baiwa matasan Najeriya, shawara da kada su kuntata tunanin su na cewa, sai wane ko wane ke iya samun damar kara karatu, domin nasara daga Allah take. Ya dai jawo hankalin matasa a kowane mataki da su dage matuka, sannan su bar ma Allah saura.