Shahararren kamfanin sada zumunta na yanar gizo Facebook, sun kammala sa hannu a wata sabuwar yarjejeniya da wani kamfanin, a yunkurin sun a samar da tsarin wuta daga iska ko hasken rana. Tsarin dai zai ba kamfanin damar dogaro da kansu, wajen samar da wuta da zata bada wuta ga sabon dakin ajiye bayanai dake karamar hukumar Dixon a jihar Nebraska.
Sabuwar cibiyar, da za’a dinga watsa bayanai a ko ina a fadin duniya, na bukatar wuta da karfin ta ya kai megawat 200, wanda za’a samar daga wasu fankoki masu juyawa don samar da wutar lantarki.
Karfin wutar da cibiyar zata samar, sai ya kai kimanin megawat 320, wanda sauran megawat 120, za’a siyar ma jama’a mabukata a karamar hukumar. A cewar kamfanin wannan sabuwar cibiyar zata zama ta biyu mafi girma, wajen samar da wuta a jihar.
Ana dai sa ran sauran wutar zata wadatar da sama da gidaje 90,000, a tabakin mai magana da yawun kamfanin Mr. David Bracht, nan da sabuwar shekara mai zuwa 2018, kamfanin na facebook zasu dinga samarda wutar su daga tsarin samar da tsaftattaciyar wuta daga hasken rana ko iska.